Account

Posts of Datti Assalafiy Tech

newest first

#1720Link preview
Views27,300+438%vs avg
Forwards—
Reactions81
Comments—
#1712Link preview
Views17,700+249%vs avg
Forwards—
Reactions29
Comments—
#1710Text

PI NETWORK YA SHIGA GOGAYYA DA SU APPLE, GOOGLE DA MICROSOFT!!! Abubuwa uku mahimmai da pi network ta gabatar a jiya ranar bikin Pi2day🔥 Yayin da mafi yawancin mutane a cikin harkar Crypto suke zuba ido suna jiran ganin farashin Pi yayi tashin gwauron zabi, su kuwa Pi Core Team babban shiri suka fito da shi na yadda Pi zai zama babban jigo a daukacin duniyar Intanet (Web2 da Web3). A bukin Pi2Day na jiya, Core Team sun saki wasu manyan abubuwa guda uku masu girgiza duniyar crypto da internet, wadanda ke nuna cewa Pi ba wai coin na gama-gari ba ne kawai, asali ma yana so ya kafa daular da zata raba gari da su Apple, Google, da Microsoft Ga muhimman abubuwa guda uku da ya kamata kowane Pioneer ya sani: 👇 (1) SOLO HOST (Juya Kwamfutarka ta Zama Supercomputer) 💻 Wannan wani sabon tsari ne a Pi Desktop (na kwamfuta) wanda zai baiwa masu ƙera manhajoji (Developers) damar kawo apps na AI (Artificial Intelligence) da manhajar raba karfin kwamfuta (Distributed Computing). Kamar yadda mutane ke amfani da kwamfutar su wajen gudanar da Node na Pi, yanzu zasu iya amfani da ita wajen gudanar da manhajar AI (misali kamar wani app da ake ƙira Hermes). Sirrinka da bayananka suna nan a kwamfutarka ba tare da sun tafi uwar garken (server) wani kamfani ba. Wannan kalubale ne ga Manyan Kamfanoni, saboda irin su Google da Microsoft suna kashe biliyoyin daloli wajen gina "Cloud Servers" na AI. Amma Pi yana so ya hada ƙarfin kwamfutoci sama da 420,000 na Pioneers don su zama babbar kwamfuta guda ɗaya ta duniya ba tare da mallakar wani babban server ba. (2) PI SIGN-IN (Mabudin Intanet Kamar "Sign in with Google") 🔑🌐 Wannan tsari ne da zai ba ka damar amfani da asusunka na Pi (Pi Account) wajen yin rajista ko shiga (Login) a sauran jafar yanar gizo (websites) da apps na waje da ba na Pi ba, ba sai ka tsaya kana ƙirƙirar sabon password ko username a kowane website ba. Da zarar ka danna "Sign in with Pi," ka shiga ke nan cikin sauƙi ta hanyar amfani da Pi Browser dinka. Kamar yadda kake gani ana sa "Sign in with Google" ko "Apple" a kafar yanar gizo, yanzu Pi ya shigo wannan sa'ar. Bambancin shi ne, Pi yana zuwa ne da asusun da aka tabbatar na mutum ne da aka tantance (bashi da bot ko fake accounts), kuma yana da alaƙa da Pi Wallet don biyan kuɗi na gaba, ba kamar yadda a Google zaka buɗe account barkatai kai kaɗai ba. (3) PI VERIFY (Zama Kamfanin Tantance Mutane Na Duniya) Pi Network ya buɗe tsarin sa na KYC (tantance bil'adama) ga sauran kamfanonin waje da bankuna na intanet (Fintechs) wadanda suke bukatar tantance mambobinsu. Kamfanonin waje zasu rika amfani da fasahar Pi wajen gano mutanen gaskiya domin magance zamba da fake accounts. Kuma babban abin farin cikin shi ne, Wadannan kamfanoni na waje zasu rika biyan kudi ne da Pi Coin domin amfani da wannan service ɗin na PiVerify. Pi ya riga ya tantance mutane sama da miliyan 18 a kasashe sama da 200. Yanzu Pi ya daina zama mai neman KYC, ya koma shi ne mai bayar da KYC (KYC Provider) ga duniya. Wannan zai kawo babban sauyi Na use case (utility) da bukatar Pi Coin a kasuwa ta zahiri. Yayin da muke ke jiran yaushe za a bude Mainnet ko nawa ne farashi?, mu sani cewa darajar crypto tana ginuwa ne akan amfaninta (Utility). Pi Core Team suna aiki ta ƙuru wajen faɗaɗa utility da use case, suna gina ababen more rayuwa ne na intanet wanda zai tilasta wa manyan kamfanoni amfani da shi. Idan Pi ya zama shi ne mabudin shiga websites, shi ne mai bada karfin AI, kuma shi ne mai tantance mutane a duniya... To batun farashi lokaci ne kawai in sha Allah. Babagana Aisami✍️ Allah Ya tabbatar mana da alherin Pi, Allah Ya sa muna daga cikin wadanda zasu amfana mu kuma amfani al'umma🙏

Open in Telegram
Views19,100+276%vs avg
Forwards—
Reactions85
Comments—
#1709Link preview
Views21,900+332%vs avg
Forwards—
Reactions189
Comments—
#1706Link preview
Views39,100+670%vs avg
Forwards—
Reactions71
Comments—
#1704Text

PI NETWORK SUN FARA SECOND MIGRATION Tun kusan sati uku da suka wuce Pi Network suka fara second migration zuwa wallet, wato a wannan second migration din suna hadawa da bonus na yawan referral dinka da suka tsallake KYC da bonus na security circle Sannan wadanda basu samu first migration ba zasu samu matukar sun cika ka'ida, kuma Pi Network sunce zasu fifita first migration akan second migration Pi network suna ta nanata maganar cewa kafin mutum ya samu second migration na Pi dinsa sai ya saita 2FA, shine ka daura email address dinka a kan Pi da kake mining, da kuma confirming wallet a mainnet checklist step 3 Sun kawo wannan tsarin ne saboda su tsare dukiyar mutane daga sharrin scammers A halin da ake ciki wasu har sun fara samun second migration na Pi din su, don haka ayi kokarin cika ka'idar da suka gindaya Wadanda suka batar da Passphrase dinsu suna da damar da zasu canza wani kafin a tura musu first ko second migration Sannan a kula, akwai wasu scammers sun kirkiri wani website suna cewa a shiga ayi 2FA a cikinsa, duk inda kuka gani kar ku shiga Muna sake karfafa gwiwar Pioneers din mu, kar ku sayar da Pi dinku, idan bukata ta kama; ku sayar da rabi ku ajiye rabin abinda kuka samu zuwa nan gaba ku sha mamaki Duk bayanin da kake nema a kan Pi, tun daga kan yadda ake register, yadda ake mining, yadda ake KYC, yadda ake creating wallet, yadda ake saita 2FA, yadda ake kammala mainnet checklist step 1 zuwa 9 da sauransu, idan kaje YouTube kayi tambaya da yaren da kake fahimta za'a nuna maka bidiyo Allah Ka tabbatar mana da alheri, Ka kare mana Pi din mu

Open in Telegram
Views34,500+580%vs avg
Forwards—
Reactions112
Comments—
#1703Link preview
Views22,400+341%vs avg
Forwards—
Reactions42
Comments—