Account
Datti Assalafiy Tech

Datti Assalafiy Tech

BismilLahi Tawakkaltu alalLah Wa la haula wala Quwwata illa bilLah๐Ÿ™

Username
@dattiassalafiytech
Category
Blogs
Country
NigeriaNigeria
Subscribers71,305
Avg views per post, 7d5,650last 7 days
ERR7.92%last 7 days

Latest posts

#1724Video
Views5,780+2%vs avg
Forwardsโ€”
Reactions259
Commentsโ€”
Views growthHide views growth

Views growth

Hours after publication

Show as table
Hours after publicationViews
0 h0
16 h5,220
28 h5,780
  1. After 24 hours5,780
  2. Total to date5,780
#1720Link preview
Views27,300+383%vs avg
Forwardsโ€”
Reactions81
Commentsโ€”
#1712Link preview
Views17,700+213%vs avg
Forwardsโ€”
Reactions29
Commentsโ€”
#1710Text

PI NETWORK YA SHIGA GOGAYYA DA SU APPLE, GOOGLE DA MICROSOFT!!! Abubuwa uku mahimmai da pi network ta gabatar a jiya ranar bikin Pi2day๐Ÿ”ฅ Yayin da mafi yawancin mutane a cikin harkar Crypto suke zuba ido suna jiran ganin farashin Pi yayi tashin gwauron zabi, su kuwa Pi Core Team babban shiri suka fito da shi na yadda Pi zai zama babban jigo a daukacin duniyar Intanet (Web2 da Web3). A bukin Pi2Day na jiya, Core Team sun saki wasu manyan abubuwa guda uku masu girgiza duniyar crypto da internet, wadanda ke nuna cewa Pi ba wai coin na gama-gari ba ne kawai, asali ma yana so ya kafa daular da zata raba gari da su Apple, Google, da Microsoft Ga muhimman abubuwa guda uku da ya kamata kowane Pioneer ya sani: ๐Ÿ‘‡ (1) SOLO HOST (Juya Kwamfutarka ta Zama Supercomputer) ๐Ÿ’ป Wannan wani sabon tsari ne a Pi Desktop (na kwamfuta) wanda zai baiwa masu ฦ™era manhajoji (Developers) damar kawo apps na AI (Artificial Intelligence) da manhajar raba karfin kwamfuta (Distributed Computing). Kamar yadda mutane ke amfani da kwamfutar su wajen gudanar da Node na Pi, yanzu zasu iya amfani da ita wajen gudanar da manhajar AI (misali kamar wani app da ake ฦ™ira Hermes). Sirrinka da bayananka suna nan a kwamfutarka ba tare da sun tafi uwar garken (server) wani kamfani ba. Wannan kalubale ne ga Manyan Kamfanoni, saboda irin su Google da Microsoft suna kashe biliyoyin daloli wajen gina "Cloud Servers" na AI. Amma Pi yana so ya hada ฦ™arfin kwamfutoci sama da 420,000 na Pioneers don su zama babbar kwamfuta guda ษ—aya ta duniya ba tare da mallakar wani babban server ba. (2) PI SIGN-IN (Mabudin Intanet Kamar "Sign in with Google") ๐Ÿ”‘๐ŸŒ Wannan tsari ne da zai ba ka damar amfani da asusunka na Pi (Pi Account) wajen yin rajista ko shiga (Login) a sauran jafar yanar gizo (websites) da apps na waje da ba na Pi ba, ba sai ka tsaya kana ฦ™irฦ™irar sabon password ko username a kowane website ba. Da zarar ka danna "Sign in with Pi," ka shiga ke nan cikin sauฦ™i ta hanyar amfani da Pi Browser dinka. Kamar yadda kake gani ana sa "Sign in with Google" ko "Apple" a kafar yanar gizo, yanzu Pi ya shigo wannan sa'ar. Bambancin shi ne, Pi yana zuwa ne da asusun da aka tabbatar na mutum ne da aka tantance (bashi da bot ko fake accounts), kuma yana da alaฦ™a da Pi Wallet don biyan kuษ—i na gaba, ba kamar yadda a Google zaka buษ—e account barkatai kai kaษ—ai ba. (3) PI VERIFY (Zama Kamfanin Tantance Mutane Na Duniya) Pi Network ya buษ—e tsarin sa na KYC (tantance bil'adama) ga sauran kamfanonin waje da bankuna na intanet (Fintechs) wadanda suke bukatar tantance mambobinsu. Kamfanonin waje zasu rika amfani da fasahar Pi wajen gano mutanen gaskiya domin magance zamba da fake accounts. Kuma babban abin farin cikin shi ne, Wadannan kamfanoni na waje zasu rika biyan kudi ne da Pi Coin domin amfani da wannan service ษ—in na PiVerify. Pi ya riga ya tantance mutane sama da miliyan 18 a kasashe sama da 200. Yanzu Pi ya daina zama mai neman KYC, ya koma shi ne mai bayar da KYC (KYC Provider) ga duniya. Wannan zai kawo babban sauyi Na use case (utility) da bukatar Pi Coin a kasuwa ta zahiri. Yayin da muke ke jiran yaushe za a bude Mainnet ko nawa ne farashi?, mu sani cewa darajar crypto tana ginuwa ne akan amfaninta (Utility). Pi Core Team suna aiki ta ฦ™uru wajen faษ—aษ—a utility da use case, suna gina ababen more rayuwa ne na intanet wanda zai tilasta wa manyan kamfanoni amfani da shi. Idan Pi ya zama shi ne mabudin shiga websites, shi ne mai bada karfin AI, kuma shi ne mai tantance mutane a duniya... To batun farashi lokaci ne kawai in sha Allah. Babagana Aisamiโœ๏ธ Allah Ya tabbatar mana da alherin Pi, Allah Ya sa muna daga cikin wadanda zasu amfana mu kuma amfani al'umma๐Ÿ™

Open in Telegram
Views19,100+238%vs avg
Forwardsโ€”
Reactions85
Commentsโ€”

All posts

Connections